Wasu kungiyoyin fararen hula a Jihar Zamfara, sun shigar da kamfanonin sadarwa kara gaban Babbar Kotun Jihar bisa ci gaba da rufe hanyoyin sadarwa a Jihar.
Kungiyoyin, karkashin inuwar ‘Zamfara Cycle Community Initiative’ na zargin kamfanonin ne da saba yarjejeniya tsakaninsu da masu hulda da su a Jihar.
- Kaduna: ’Yan bindiga sun harbe basarake a Giwa, kwana 1 bayan kashe mutum 38
- Yadda ake karbar cin hanci a Gwamnatin Buhari
Sun ce ci gaba da rufe layukan sadarwa a Jihar ya jefa miliyoyin jama’arta cikin halin kaka-ni-ka-yi, kuma suna neman kotun ta raba musu gardama kan ko suna da damar neman a biya su diyyar asarar da suka tafka a sakamakon haka.
A cewarsu, kamfanonin da suke kara sun rufe dukkan hanyoyin sadarwa a fadin Jihar tun ranar uku ga watan Satumban 2021, ba tare da samun izinin yin hakan ba daga kotu.
Yanzu haka dai, shida daga cikin Kananan Hukumomin Jihar 14 layukan sadarwarsu a kulle suke.
A cikin kunshin karar dai da kungiyoyin suka shigar ranar Litinin, ta hannun lauyoyinsu, Musa Umar da Ahmed Jamilu, sun yi ikirarin cewa matakin ya saba da yarjejeniyar da kamfanonin MTN da Glo da Airtel da kuma 9mobile suka kulla da su.
Kazalika, daga cikin wadanda ake karar har da Gwamnan Jihar ta Zamfara, da Babban Lauyan Gwamnatin Jihar, kuma Kwamishinan Shari’a da kuma Hukumar Kula da Kamfanonin Sadarwa ta Kasa (NCC).
Sun shigar da karar ne bisa dogaro da doka ta 15, sadara ta 3 (1) na Kundin Dokokin Jihar Zamfara na 2014, da kuma sassa na 96 da 97 da 98 da kuma 99 na Dokokin ’Yancin Fararen Hula na shekarar 2004.