Wata Kotun Majistare da ke Karu a Abuja, ta gurfanar da wani mutum da ake zargin ya lakada wa wata mata mai juna biyu har sai da ta yi bari.
Mutumin dai ana zarginsa ne da aikata laifukan cin zarafi, da amfani da karfin da ya haddasa wa matar barar da dan tayin da ke cikinta.
- Yawan tsararrun da ke Jiran shari’a ne silar hare-hare a gidajen yari —Kungiya
- Wakokin Taylor Swift 10 sun shiga sahun goman farko a ‘BillBoard’
Dan Sanda mai gabatar da kara, Olarewaju Osho ya bayyana wa kotun cewa, tun a watan Satumba ne a mutumin ya naushi matar a ciki a tashar motar Karu.
Osho ya ce haka ya janyo wa matar ta yi barin cikinta, kuma laifin ya saba wa sashi na 365 na kundin Penal Code.
Sai dai wanda ake zargi ya musanta, inda Alkalin kotun Hassan Mohammed ya ba da belinsa kan N100,000 tare da gabatar da mai tsaya masa wanda ya mallaki katin shaidar dan kasa kuma ya mallaki fasfo na tafiye-tafiye zuwa ketare.
Baya ga haka, ya umarce shi da ya sanya hannu kan takardar rantsuwar ba zai sake shiga hurumin matar ba, sannan da dage shari’ar zuwa ranar 9 ga wata Nuwamba.