Wasu ’yan daba sun yi wa Mataimakin Firinsifal na wata makarantar sakandare dukan tsiya a wani mummunan harin da suka kai masa saboda ya hana wani ɗalibi satar jarabawa.
A yayin da ake ci gaba da jarabawar kammala sakandare ta WASSCE da ake yi a halin yanzu ne, Mista Rotifa, mataimakin shugaban wata makaranta mai zaman kanta mai suna Child Development College da ke Akure, hedikwatar Jihar Ondo, ya hana ɗalibin satar amsa.
Bayan haka ne ’yan daban sun tsare Mista Rotifa suka yi masa dukan kawo wuƙa bayan sun jawo shi daga motar ’yan sanda, kafin a ceto shi a kai shi asibiti.
Lamarin ya faru ne bayan Mista Rotifa ya ƙwace wayar salula da wani ɗalibi ke amfani da ita wajen yin satar jarabawa makon jiya.
Majiyoyi sun yi zargin cewa iyayen ɗalibin ne suka ɗauko hayar ’yan daban, bayan wata barazana da mahaifiyar ɗalibin ta yi a baya cewa za ta kai hari ga duk wanda ya hana ɗanta yin satar jarabawa.
Duk da barazanar ta farko, an ruwaito cewa makarantar ba ta ɗauki wani mataki ba har sai da aka kawo wa Mataimakin Firinsifal ɗin farmaki.
’Yan daban sun tsare Mista Rotifa sa’annan suka yi masa dukan tsiya bayan ya kai rahoton barazanar ga ’yan sanda. Sun jawo shi daga motar ’yan sanda kuma suka dake shi kafin a ceto shi a kai shi asibiti.
Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Ondo ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa an fara bincike.
Ko da yake an sallame shi daga asibiti, Mista Rotifa bai koma gida ba saboda tsaron lafiyarsa.
Hukumomi suna ƙoƙarin kama masu hannu a laifin kuma ana shirye-shiryen tabbatar da tsaron ma’aikatan makarantar da ɗalibai har zuwa ƙarshen jarabawar WASSCE.