Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da ’Yan Ci-rani ta Duniya (IOM) a ranar Talata sun kwaso wasu ’yan Najeriya kimanin 151 da ke gararamba a birnin Benghazi na kasar Libya.
Jami’in ofishin jakadancin Najeriya da ke Libya, Kabiru Musa ne ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwar da ya ba Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja ranar Talata.
- DAGA LARABA: Me ya sa ‘yan siyasa ke kin yarda da shan kaye a zabe?
- HOTUNA: NNPC ya fara hako mai a Nasarawa
Ya ce daga cikin mutanen, 71 mata ne, 54 maza, sai kananan yara 14 da jarirai 13, kuma tuni suka sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas da misalin karfe 8:00 na dare.
Ya ce ko a shakara ta 2022, sai da IOM da hadin gwiwar Ma’aikatar Harkokin Waje ta Najeriya suka sami nasarar kwaso ’yan Najeriya kimanin 4,000, wadanda ke zaune a kasar ba bisa ka’ida ba.
Ya ce mutanen da aka kwaso na ranar Talata su ne rukunin farko a bana, kuma suna sa ran kwaso wasu da dama a nan gaba kadan.
Kabiru ya kuma ce ranar Laraba za a kara kwaso wasu karin ’yan najeriyar daga birnin Tripoli, yayin da ake sa ran sake kwaso wasu ranar 3 ga watan Afrilu daga birnin misrata, duka a Libyan. (NAN)