✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kwaso karin ’yan Najeriya 327 daga Birtaniya

’Yan Najeriya 327 da suka makale a Birtaniya bayan kullen coronavirus sun baro birnin London zuwa gida ranar Lahadi. Jami’ar Hulda da Jama’a ta Ministan…

’Yan Najeriya 327 da suka makale a Birtaniya bayan kullen coronavirus sun baro birnin London zuwa gida ranar Lahadi.

Jami’ar Hulda da Jama’a ta Ministan Harkoin Wajen, Sarah Sanda ta ce mutanen da suka taso daga filin jirgi na Gatwick, London, za su sauka ne a Abuja.

Sarah Sanda ta ce “sun baro London da misalin 11.15 na safiyar Lahadi 9 ga Agusta, a cikin jirgin kamfanin Air Peace”.

Tun bayan sassauta kullen COVID-19 Gwamnatin Tarayya ke ta kwaso ’yan Najeriya da suka makale a wasu kasashe zuwa gida.

Ko a ranar Asabar gwamnati ta kwaso wasu mutum 323 daga Birtaniyan wadanda ta sauke su a Legas.

Akan tantance dukkannin wadanda aka kwaso din sannan a killace su na mako biyu domin tabbatar da ba su harbu da cutar ba kafin su koma ga iyalansu.