✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kusan ba hammata kan Trump a Majalisar Dattawan Amurka

Majalisar Dattawan Amurka ta amince da wasu ka’idoji da aka gindaya kan fara sauraron bahasin da zai iya kaiwa ga tsige Shugaba Donald Trump bayan…

Majalisar Dattawan Amurka ta amince da wasu ka’idoji da aka gindaya kan fara sauraron bahasin da zai iya kaiwa ga tsige Shugaba Donald Trump bayan shafe kusan sa’o’i 13 ana tafka muhawara a ranar farko.

Masu gabatar da kara na Jam’iyyar Democrat sun kusa su bai wa hammata iska da lauyoyin Trump game da zaman sauraren bahasin, yayin da ’ya’yan Jam’iyyar Republican suka nuna kin amincewa da bukatar a gabatar da shaidu fiye da daya.

A ranar Talata ce Majalisar Dattawan Amurka ta fara zaman muhawara kan batun tsige Shugaba Donald Trump, kamar yadda Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar, Mista Mitch McConnell, ya sanar a makon jiya.

Majalisar wadda ’yan Jam’iyyar Republican ke da rinjaye a cikinta, ta fara muhawara kan wannan batu ne bayan Majalisar Wakilai da Democrat ke da rinjaye ta amince da tsige Shugaban. Ana tuhumar Trump da bukatar Shugaban Ukraine ya yi katsalanda a zaben Amurka da kuma amfani da ikonsa ta hanyar da ba ta dace ba.

Shugaba Trump ya zama Shugaban Amurka na uku a tarihi da zai gurfana a gaban ’yan majalisar kasar, bisa tuhumar aikata laifuffukan da za su kai ga tsige shi. Sai dai wadansu magoya bayansa da shi kansa na ganin zai yi wahala yunkurin tsige shi ya kai ga  nasara.

 

…Lauyoyin Trump sun bayar da hanzarinsu

Lauyoyin Fadar White House sun mika hujjojin da za su kare Shugaba Donald Trump a bahasin da Majalisar Dattawa ta fara saurara, kan shirin tsige shi daga mukaminsa.

Lauyoyin sun gabatar da hanzarin nasu ne kwana daya kafin a fara sauraren bahasin a gaban majalisar ranar Talata. A wani takaitaccen martanin farko kan tuhume-tuhumen da Majalisar Wakilai ta amince da su, Lauya Pat Cipollone da Jay Sekolow sun nemi Majalisar Dattawan ta yi watsi da tuhume-tuhumen da ake yi wa Trump saboda a cewarsu, “Za su iya zama hadari ga kundin tsarin mulkin Amurka tare da yin mummunar tasiri ga tsarin gwamnati.”

Lauyoyin sun  kalubalanci Majalisar Wakilan cewa tana kokari rage karfin ikon Shugaban ne game da damar da doka ta ba shi kan manufofin kasashen waje. Sun kara da cewa, Majalisar Wakilan na kokarin hukunta Bangaren Zartarwa ne, saboda ya yi amfani da ikon da doka ta ba shi na gudanar da ayyukansa.