✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kusa ci gaba da haska shirin Labarina —Aminu Saira

"Nan da makwanni kadan za mu sanar da lokacin da za a dawo," inji Daraktan shirin.

Fitaccen darakta a masana’antar Kannywood, kuma daraktan shirin Labarina mai dogon zango, Aminu Saira ya bayyana cewa an kusa dawowa domin ci gaba da haska shirin.

Shi dai wannan shirin mai dogon zango na Labarina, ya dauki hankalin mutane da dama, ciki har da manyan mutane da a baya ba kasafai suke shiga lamarin fina-finan Hausa ba.

Aminu Saira ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa, “Ma sha Allah, cikin yardar Ubangiji, mun samu damar daukar fiye da kashi 70 na shirin Labarina zango na uku.

“In sha Allah da zarar mun kammala dauka nan da makwanni kadan za mu sanar da lokacin da za a dawo, da kuma inda za a ci gaba da haska muku shi. Muna godiya da soyayyarku a gare mu.”

Idan ba a manta ba, Aminiya ta ruwaito bayan tafiya hutun da suka yi bayan kammala haska zango ma biyu na shirin, mutane da dama sun yi ta magana tare da kasancewa cikin jiran ranar da za a ci gaba da haska shirin da kuma inda za a haska shi.