✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kubutar da matar da aka kulle a daki shekara 2 a Kaduna

A ranar Litinin din nan ne aka gano wata mata da ‘yan uwanta suka rufe ta a cikin daki kusan shekaru biyu saboda kurum wai…

A ranar Litinin din nan ne aka gano wata mata da ‘yan uwanta suka rufe ta a cikin daki kusan shekaru biyu saboda kurum wai tana san komawa wajen tsohon mijinta a Rigasa da ke a Karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

Matar mai Suna Hassana Saleh, ana zargin wai ‘ya’yanta mai Suna Lawal Saleh ne ya rufe ta a daki na tsawon shekaru a dakin inda aka ce take fitsari da kuma kashi har da cin abinci duk a ciki‎.

Wakilinmu ya samu labarin cewa sai da ‘yan sanda suka yi amfani da wani karfe wajen balle kwadon da aka yi amfani da shi wajen rufe dakin da take ciki wanda kuma ke da duhu.

Wata Gidauniya mai Suna Arida ‎ne suka gano Hassana a inda aka kulle ta bayan samun labarin halin da take ciki a tsawon wannan shekaru biyu. Shugaban Gidauniyar Hajiya Rabi Salisu Ibrahim wacce tana cikin wadanda suka ceto Hassana ta ce, wai yayan Hassana watau Lawal Saleh ya ce, sun rufeta a dakin ne saboda nacewa da ta yi sai ta koma gidan mijinta.

Ta kara da cewa, dakin ita matar a ganin su mijinta baya kaunarta wanda hakan yasa ya saketa wanda a cewarsu sakin ne ya jefata cikin damuwa.

Shugabar Gidan marayu ta Arrida-Foundation Kaduna Hajiya Rabi Salisu Ibrahim tare da Hassanah Saleh da aka ceto.