✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kori sojoji 3 saboda laifin garkuwa da mutane a Borno

Rundunar sojojin Najeriya ta ce, ta kori wasu sojoji da aka kama da laifin garkuwa da mutane a wajen garin Maiduguri babban birnin jihar Borno.…

Rundunar sojojin Najeriya ta ce, ta kori wasu sojoji da aka kama da laifin garkuwa da mutane a wajen garin Maiduguri babban birnin jihar Borno.

Kwamandan rundunar sojojin Operation Lafiya Dole, Manjo Janaral Olusegun Adeniyi, ne ya bayyana haka a garin na Maiduguri a lokacin da yake mika korarrun sojojijin ga rundunar ‘Yan sanda domin fuskantar hukunci.

Manjo Janaral Olusegun, ya ce sun kama sojojin ne cikin gun-gun masu garkuwa da mutane su 22, a cikin wani gini a yankin Maiduguri.

Ya kara da cewa, su dai wadannan sojoji an tura su aiki ne karkashin rundunar ta Operation Lafiya Dole, yayin da daga bisani suka bige da shiga cikin batagari don aikata mummunan laifi na satar mutane, fashi da makami da kuma tsafe-tsafe.