✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kori Ministan Lafiyar Zambia daga aiki

Zargin almundahana ya dabaibaye ma'aikatar lafiyar a tsawon lokaci

Shugaban Kasar Zambia, Edgar Lungu ya sallami Ministan Lafiya, Chitalu Chilufya, daga ma’aikatar da zargin almundaha ya dabaibaye.

A ranar Lahadi Shugaban Kasar ya sanar da sallamar Ministan nan take cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

“Na sallami Dokta Chitalu Chilufya daga Matsayin Ministan Lafiya nan take na kuma nada Dokta Jonas Kamima Chanda, dan Majalisa mai wakiltar Bwana Mkubwa a Mai’akatar”, inji shi.

Sai dai sakon Shugaban Kasar bai bayyana dalilin daukar matakin ba, sai dai zargin rashawa ya dabaibaye Ma’aikatar Lifayar.

Karami daga ciki zarge-zargen shi ne da na badakalar Dala miliyan 17 na sayo kwaororon roba da kuma safar kariya a ma’aikatar.

A watan Yunin 2020 an tsare Minsta Chilufya saboda zargin rashawa da mallakar kadarori da haramtattun kudade.

Daga baya rashin hujjoji ya sa aka wanke shi ya kuma ci gaba da aikinsa na Ministan Lafiya.

Sai dai shugaban ’yan adawa, Hakainde Hichilema ya ce, “Sallamar Chitalu Chilufya ba zai yi wani tasiri ba kuma ya zo a makare”.