A ranar Talata Hukumar Kula da Aikin Dan Sanda (PSC) ta kori mayan jami’an ’yan sanda bakwai daga aiki tare da rage wa wasu 1o matsayi saboda aikaa ba daidai ba.
Hukumar ta dauki wannan mataki ne yayin ci gaba da babban taronta karo na 15 wanda ake sa ran kammalawa ya zuwa ranar Alhamis.
- Ranar Juma’a Buhari Zai Gabatar Da Kasafin 2023 Ga Majalisa
- Mutum 9 ’yan gida daya sun mutu bayan cin abinci
Kakakin hukumar, Ikechukwu Ani, ta shaida wa ’yan jarida wadanda lamarin ya shafa sun hada da masu mukamin CSP daya da SP daya da kuma ASP biyar.
Wadanda aka rage wa matsayi sun hada da mutum daya daga CSP zuwa SP, uku daga SP zuwa DSP, biu daga DSP zuwa ASP, hudu daga ASP zuwa Sufeto da dai sauransu.
Taron, wanda ke gudana karkashin jagorancin mukaddashin shugaban hukumar, Mai Shari’a Clara Ogunbiyi, an gabatar masa da korafi kan laifuffuka 47 da ake zargin ’yan sanda sun aikata, domin daukar matakin da ya dace.
Haka nan, taron ya saurari daukaka karar da wasu ’yan sanda da aka kora daga aiki suka yi.
Kakakin hukumar, Ikechukwu Ani, ta shaida wa ’yan jarida wadanda lamarin ya shafa sun hada da masu mukamin CSP daya da SP daya da kuma ASP biyar.
Wadanda aka rage wa matsayi sun hada da mutum daya daga CSP zuwa SP, uku daga SP zuwa DSP, biu daga DSP zuwa ASP, hudu daga ASP zuwa Sufeto da dai sauransu.
Hukumar ta ja hankalin ’yan sanda da su rika gudanar da ayyukansu daidai da doka, tana mai cewa za ta nuna halin ba-sani-ba-sabo wajen daukar matakin kan duk wanda aka kama da take doka.