Masu garkuwa da mutane sun sace akalla mutum 14 a cikin mako daya domin karbar kudin fansa a Jihar Kuros Riba.
Bayanan da Aminiya ta samu sun nuna cewa mutum tara aka fara sacewa, sannan aka sace sauran daga baya.
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Kamata Ku Sani Kan Sabbin Kudaden Najeriya
- Mun daina bai wa miyagun ’yan siyasar Najeriya biza —Birtaniya
Lamarin ya faru ne a kan babbar hanyar Ikom zuwa Kalaba a tsakanin garin Akamkpa zuwa Uyanga a Jihar Kuros Riba, wacce take daya daga cikin jihohin kasar nan da ba a cika samun garkuwa da mutane ba.
Sai dai Aminiya ta samu labarin cewa yanzu lamarin garkuwa da mutane ya fara kamari a jihar, inda ake samun matsalolin a wasu bangarori.
Daga cikin wadanda aka sace, akwai wasu likitoci biyu a Kalaba, babban birnin jihar, lamarin da ya sa kungiyar likitocin jihar ta shiga cikin tashin hankali.
Shugaban Kungiyar Likitoci ta Kasa reshen jihar ta Kuros Riba, Dokta Felis Archibong, ya shaida wa wakilinmu damuwarsu da jimamin rashin sanin halin da abonkan aikinsu ke ciki.
Ya yi bayanin cewa masu garkuwa da likitoci sun kira iyalan daya daga cikin likitocin sun bukaci a ba su Naira miliyan 60.
Ganin yadda matsalar ta fara yawaita a jihar ce, ya sa gwamnan jihar Farfesa Ben Ayade, ya fitar da sanarwar cewa ba zai bari masu wannan muguwar dabi’a su ci karensu babu babbaka a jiharsa ba.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Irene Ugbo, ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce rundunar ta tura jami’anta inda aka samu matsala, sannan sun kubutar da mutum takwas ciki har da mata uku sannan sun kashe masu garkuwa uku.