✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kona wani bangare na kamfanin dangote a Habasha

Masu zanga-zanga sun kona motoci da wasu kayan aiki a kamfanin siminti na Alhaji Aliko dangote da ke yankin Oromia a kasar Habasha.Masu boren dai…

Masu zanga-zanga sun kona motoci da wasu kayan aiki a kamfanin siminti na Alhaji Aliko dangote da ke yankin Oromia a kasar Habasha.
Masu boren dai na nuna rashin amincewa ne da kisan akalla mutum 55 a wani turmutsitsin da aka yi a wajen wani bikin addini da aka yi a ranar Lahadin da ta gabata, kamar yadda kafar labarai BBC ta bayyana.
Wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar ta tabbatar da aukuwar lamarin.
Wasu rahotanni na cewa an kona wani caji ofis tare da sakin fursunoni a lokacin zanga-zangar a yankin Bule Hora.
Masu fafutika sun ce dakarun tsaron kasar sun bude wuta a kan masu bikin bayan sun rera wakar bukatar neman ’yancin siyasa. Abin da gwamnatin ta musanta.
dangote shi ne mutumin da ya fi kowa arziki a Nahiyar Afirka kuma yana da kamfanoni da masana’antu a kasashe da dama a sassan nahiyar.
 A shekaranjiya Laraba an toshe hanyoyin sadarwa na Intanet a fadin kasar Habasha a daidai lokacin da ’yan kasar ke ci gaba da zanga-zangar adawa da gwamnati. Ba a dai ba da dalilin toshe intanet din a hukumance ba.
A baya gwamnati ta zargi ’yan adawa da suke zaune a kasashen waje da yin amfani da kafafen sada zumunta na Facebook da Twitter wajen shirya zanga-zanga a kasar.