✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kona tan 402 na lalatattu da jabun kayayyaki a Kano

A cewar hukumar, nan ba da jimawa ba za ta gurfanar da masu kayan a gaban kotu domin su girbi abin da suka shuka.

Hukumar Kula da Hakkin Masu Sayen Kaya ta Jihar Kano (KSCPC) ta kona tan 402 na jabun kayayyaki da wadanda wa’adin amfaninsu ya kare da ta kwace daga ’yan kasuwa a Jihar.

An dai kona kayan ne a shalkwatar Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) da ke Kano ranar Lahadi, kuma Gwamnan Jihar, Abdullahi Umar Ganduje ne ya jagoranci kona su.

Da yake jawabi a wurin kona kayan, mai mukaddashin Shugaban KSCPC, Baffa Babba Dan-Agundi ya ce kayayyakin sun hada da abinci da magunguna da kayan kwalliya da hatsi da taba sigari da abincin dabbobi da kuma abubuwan sha.

Lokacin da Gwamna Ganduje ke jagorantar kone kayan a Kano

Ya ce hukumar na aiki kafada da kafada da hukumomin NDLEA da Hukumar Kula da Ingancin Kayayyaki ta Najeriya (SON), Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) da Hukumar ’Yan Sandan Farin Kaya ta SSS da sauran hukumomin tsaro wajen samun nasararta.

“Saboda yawan kayan da muke kamawa, sai da hukumar NDLEA ta umarce mu da mu tsagaita haka saboda ba su da wurin ajiyewa,” inji shi.

Yadda kayayyakin ke ci da wuta yayin bikin konewar

Dan-Agundi ya kuma ce kone kayan ya zo a daidai lokacin da aka fi bukata kasancewar ko a kwanakin baya sai da jihar ta yi fama da wata bakuwar cuta mai alaka da gurbatattun kayayyaki inda sama da mutum 1,000 suka kwanta a asibiti.

Shi ma da yake jawabi, Gwamna Ganduje ya ce kone kayan alama ce ta cewa jihar na cin nasara a yakin da take yi da jabun kayayyaki.

Ya ce jihar ba aikin lalata kayan ta dukufa yi kawai ba, za kuma ta mayar da hankali wajen dakile ayyukan masu sarrafawa da shigo da irin wadannan kayayyakin.

Wasu daga cikin irin kayayyakin da hukumar ta kwace

Ganduje ya ce nan ba da jimawa ba hukumar za ta gurfanar da masu kayan a gaban kotu domin su girbi abin da suka shuka.

Taron kona kayan dai ya samu halarcin wakilan hukumomin NAFDAC da SON, da NDLEA da SSS da ma sauran jami’an tsaro da ke jihar.

%d bloggers like this: