✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kona katafariyar gonar Obasanjo

An kona itatuwan gonar mangoron Obasanjo mai fadin kadada 2,420 a Binuwai.

Wasu da ba a san ko su wane ne ba sun kai hari a gonar tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, inda suka kona amfanin gonar.

Da yake tabbatar da harin, Obasanjo ya yi tir da harin da aka kai wa gonar mangoronsa mai fadin kadada 2,420 aka lalata masa amfanin gonar ta hanyar kona itatuwan a karshen makon da ya gabata.

Gonar Obasanjon tana nan ne a kauyen Hawe da ke yankin Aliade na Karamar Hukumar Gwer ta Gabas a Jihar Binuwai.

A wata sanarwa da kakakin Obasanjo, Kehinde Akinyemi, ya fitar a garin Abeokuta na Jihar Ogun, Obasanjo ya ce kona gonar tasa da aka yi sam bai dace ba.

Ana zargin wasu zauna-gari-banza ne dai suka kona gonar mangoron ta Obasanjo kan sa-in-sa da suka samu da mazauna yankin game da biyan kudin fansar gonar wadda a baya mallakin Gwamantin Jihar Binuwai ce.

Da yake Allah wadai da barnar, Shugaban Karamar Hukumar Gwer ta Gabas, Emmanuel Ortserga, ya bayyana harin a matsayin bakin ciki, amma ya ce mutum hudu sun shiga hannu kan zargin kona gonar.

Obasanjo, ya yaba wa wadanda suka jajanta masa, ya kuma bayyana jin dadinsa cewa ba a samu asarar rai ba.