✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An koka da ’yan sintirin kungiyar Fulani a Oyo

Sarkin Fulanin Igaga a Jihar Oyo, Alhaji Salihu kadiri ya koka da yadda ƙungiyar ’yan sintiri ta Fulani ke cin zarafin Fulani makiyaya a sassan…

Sarkin Fulanin Igaga a Jihar Oyo, Alhaji Salihu kadiri ya koka da yadda ƙungiyar ’yan sintiri ta Fulani ke cin zarafin Fulani makiyaya a sassan jihar, inda  a cewarsa aikace-aikacen ƙungiyar suna wuce gona-da-iri.
Sarkin ya shaida wa Aminiya cewa irin cin kashin da ƙungiyar ta ’yan sintirin ke yi wa Fulanin yankin shi ya sa suka shigar da takardar kokensu ga Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi a kwanakin baya,,inda suka buƙaci ya binciki ayyukan kungiyar domin ceto rayukan Fulani makiyaya a yankin.
“Shugaban kungiyar Miyyati Allah reshen Jihar Oyo, Yakubu Bello ne ya kafa kungiyar ta ’yan sintiri, waɗanda suke far wa jama’ar da ba su ji ba ba su gani ba. Da zarar sun kama mutum sai su kai shi ofishinsu, su ba shi kashi sannan su yanka masa tarar maƙudan kuɗi; ta yadda suke karɓar Naira dubu 500 zuwa miliyan ɗaya. Don haka muke kira ga hukuma da ta shigo ta binciki lamarin,” inji Sarkin Fulanin.
daya daga cikin Fulanin da suka sha kashi a hannun ’yan ƙungiyar sintirin, Malam Aliyu, ya shaida wa Aminiya cewa a ranar Alhamis ɗin da ta gabata ce, bayan sun fita kasuwar Igbora shi da ƙannensa, sai aka sanar masa cewa ga ƙaninsa can ’yan sintiri sun kama shi suna dukansa. “Da muka je mu jiyo dalilinsu na dukan sai suka komo kanmu ɗauke da miyagun makamai da suka haɗa da sanduna da wuƙaƙe da bindigogi. A haka suka rufe ni da duka suka kumbura min fuska suka fasa mini kai har sai da wadansu ’yan sanda suka shiga tsakaninmu. Da ’yan sandan ba su wajen, to da sun harbe ni ko su yi garkuwa da mu,” inji shi.
Shi ma Ibrahim Salihu, wanda ɗa ne ga Sarkin Fulanin Igaga, ya shaida wa Aminiya cewa ’yan ƙungiyar sintirin sun yi garkuwa da shi a kwanakin baya. Ya ce sun iske shi ne a rumfarsa ta kasuwa suka kama shi. Da ya tambaye su laifin da ya yi kuma ina za su da shi? Sai suka ce masa kashe shi za su yi. Ya ce a haka suka tafi da shi ofishin ƙungiyar Miyyeti Allah reshen Jihar Oyo da ke garin Iseyin, bayan sun karbe masa wayoyinsa, suka lakaɗa masa duka, suka ɗaure shi har na tsawon kwana biyu.
Ya kara da cewa, a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa ofishin, sun riski wani Bafulatani a bisa babur, shi ma suka kama shi suka yi gaba da shi. Ya kuma iske wadansu Fulani da dama da aka yi garkuwa da su a ofishin yayin da wadansu ke zuwa suna biyan kuɗin tara suna karɓar ’yan uwansu. “Da suka zo kaina, sun tambaye ni iyayena? Da na shaida musu ni ɗan Sarkin Fulanin Igaga ne, nan take shugabansu, Alhaji Yakubu Bello ya ce su sake ni. Nan ya yi ta rarrashina har ya ba ni Naira 2000, ya ce na bar maganar a nan in tafi gida. A haka suke amfani da rashin gata da jahilcin da ya dabaibaye al’ummar Fulani suna cin zarafinsu, suna karɓar kuɗi a hannunsu. Kirana ga gwamnati, tun daga matakin ƙananan hukumomi har zuwa Gwamnatin Tarayya su ɗauki matakin da ya dace. Su kira taron shugabannin Fulani da na ’yan sintiri tun kafin aika-aikarsu ta kai ga tayar da tarzoma. Da yawa daga cikin ’yan sintirin tubabbun ɓarayin shanu ne da masu yin garkuwa da jama’a, domin in sun kama ɓarawo ba su miƙa shi ga hukuma sai su ce ya tuba, su ba shi Alkur’ani ya rantse. Daga nan sai su ba shi makami ya zama ɗan ƙungiya. Ai ka ga dole ya yi amfani da makamin ya ci zarafin jama’a,” inji shi.
Wakilin Aminiya ya tuntuɓi Alhaji Yakubu Bello kan koke-koken da al’ummar Fulanin ke yi a kan ƙungiyar ’yan sintiri da ya kafa, sai ya ce sun kafa ƙungiyar ce don kyautata tsaro. Ya kuma musanta zargin da ake musu na cin zarafin jama’a.