Gwamnatin jihar Zamfara ta ba da sanarwar killace iyalan marigayi Sarkin Kaura Namoda Alhaji Ahmad Muhammad Asha ta kuma yiwa fadarsa da wasu sassa na garin feshin magani.
Sarkin na Kaura Namoda dai ya rasu ne ranar Lahadi bayan ya yi fama da jinyar da ta shafi ciwon suga da hawan jini kamar yadda kanen marigayin ya shaida wa wakilinmu.
To sai dai ana rade-radin cewa marigayin ya rasu ne bayan kamuwa da ya yi da coronavirus duk da cewa hukumomi a jihar ta Zamfara ba su fito karara sun danganta mutuwar tashi da cutar ba.
Haka kuma Gwamna Muhammad Matawalle na jihar ya ba da sanarwar rufe dukkan kasuwanni da kuma dakatar da sallar jam’i a daukacin masallatai da kuma majami’u da ke fadin jihar don hana cutar ta COVID 19 ci gaba da yaduwa, kamar yadda mai ba gwamnan shawara a kan harkokin ’yan jarida Zailani Bappa ya ce.
An kuma saka dokar takaita zirga zirga daga karfe 8 na dare zuwa karfe 6 na safe a duk fadin jihar.
To amma a garin Kaura Namoda dokar za ta fara ne daga karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safe.
Daga nan sai gwamnatin ta shawarci jamar jihar da su bi umarnin da aka ba su na hana cakuduwa da kuma zama a gida domin kauce wa yada cutar.