✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kashe ’yan bindiga 5, an kama 16 a Katsina

’Yan sanda sun kwato shanun sata da miyagun kwayoyi a wurin ’yan bindigar.

’Yan sanda a Jihar Katsina sun kashe ’yan bindiga biyar suka kuma kame wasu 16 bayan musayar wuta.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya ce jami’an sun kuma kwace shanun sata 69 da wasu miyagun kwayoyi a hannun ’yan bindigar.

Ya ce an kashe ’yan bindigar ne a yayin musayar wuta da ’yan sanda a yankunan Kafur da Danja da Dutsinma da Safana da Batsari da Makera da Funtua.

An kuma kama wadansu 15 yayin musayar wutar da kuma wani matashi mai shekara 25 a kan hanyarsa ta zuwa cikin dajin da zimmar yi wa ’yan bindigar da suka ji rauni magani.

A cewar kakakin, an kwace bindigogi uku kirar gida da albarusai 10 daga hannun miyagun.