Sojojin da suka baza koma domin yaki da ‘yan ta’adda a jihar Kaduna sun hallaka ‘yan bindiga biyar a yankin Anaba da ke karamar hukumar Igabi a jihar.
Dakarun sojojin dai sun kuma ce sun kubutar da wasu mazauna kauyuka mutum tara da ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su.
- ’Yan bindiga sun far wa hanyar Kaduna zuwa Zariya
- An cafke barayin jariri mai kwanaki 3 a Kaduna
- ’Yan bindiga sun sha da kyar a hanyar Kaduna-Abuja
- Dan shekara 50 ya yi wa ‘yar shekara 6 fyade a Kaduna
Kwamishina Ma’aikatar Tsaro da Al’amuran Cikin Gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Ya ce ‘yan bindiga da dama sun tsere dauke da raunuka a jikinsu yayin gumurzu da rundunar sojin.
Ya ce mutum biyar daga cikin wadanda aka kubutar sun bayyana yadda ‘yan bindigar suka kone gawarwakin wasu ‘yan uwansu hudu.
Tuni dai aka mika mutanen tara da aka kubutar ga iyalansu.
Gwamna jihar, Malam Nasir El-Rufai ya yaba wa sojojin kan jajircewa da jarumtar da suka yi wajen ceto mutanen.