A ranar Lahadin da ta wuce ne aka kashe golan kulob din kwallon kafa na Deportivo Vida da ke Honduras Oscar Sein Munguia Zelaya a lokacin da suke tafiya tare da wani abokinsa a tsakiyar dare.
Kamar yadda mahukunta kulob din Deportivo suka tabbatar, marigayi Oscar Sein yana tare ne da wani abokinsa bayan sun ziyarci wani Otel La Ceiba don gwangwajewa, kuma a kan hanyarsu ta komawa gida ne da tsakar dare ba su ankara ba sai suka ji wani ya bude musu wuta kuma ya kashe su nan take ba tare da an kama ko an san wanda ya aikata hakan ba.
Kamar yadda kafar watsa labarai ta Mail online ta ruwaito, ta ce har lokacin hada wannan rahoto jami’an tsaro ba su samu nasarar kama ko gane wanda ya aikata wannan mummunan aiki ba.
Osacar yana daga cikin ’yan kwallon da suka buga wa kulob din sa wasa a gasar rukuni-rukuni na Honduras a karshen makon jiya inda suka lallasa kulob din Olimpia da ci 1-0, kuma wannan shi ne wasansa na karshe kafin ya gamu da ajalinsa.
Tuni mahukunta kulob din Deportivo Vida suka aika da sakon ta’aziyyarsu ga iyalan Oscar da kuma hukumar kwallon kafa ta Honduras a game da wannan al’amari da ya faru.
Idan za a tuna a kwanakin baya ne Aminiya ta ruwaito yadda aka kashe wani dan kwallon Brazil Daniel Correa Freitas a Kudancin Brazil ba tare da an san ko kama wanda ya aikata hakan ba.