✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe tsohon dan kwallon Brazil

A ranar Asabar da ta wuce ce jami’an tsaro suka tsinci gawar tsohon dan kwallon Brazil Baldiram Caetano de Morais a yashe a wani titi da…

A ranar Asabar da ta wuce ce jami’an tsaro suka tsinci gawar tsohon dan kwallon Brazil Baldiram Caetano de Morais a yashe a wani titi da ake kira Santana da ke garin Sao Poalo.

Dan kwallon wanda ya yi tashe a lokacin da yake kwallo, ya buga kwallo ne tare da tsofaffin ’yan wasan kasar irin su Romario.

Rahoton da kafar labarai ta The Mirror ta kalato, ya ce marigayin ya yi suna wajen iya kwallo, hasali ma yana daga cikin ’yan kwallon da suka fi yawan zura kwallo a raga ga kasar Brazil kafin ya yi ritaya.  Sai dai bayanai sun nuna bayan ya daina kwallo ya tsunduma harkar safarar miyagun kwayoyi da hakan ta sa ya yi kaurin suna.

Rahoton ya ce ana kyautata zaton abokan huldarsa ne suka kashe shi, inda suka bar gawarsa a yashe a kan titi kafin jami’an tsaro su gano ta.

Jami’an tsaro sun tabbatar da kama wadansu mutum uku, bisa zarginsu da hannu a kisan Baldiram amma sun ce tuni suka saki daya daga ciki saboda rashin kwakkwarar hujja.

Marigayi Baldiram ya rasu  yana da shekara 36.

Al’amarin safarar miyagun kwayoyi da aikata ta’addanci  sun yi kamari a Brazil, inda da wuya a wayi gari ba a samu labarin an kashe wani ko wasu a wani sashe na kasar ba.