A ranar Lahadi ne ’yan bindigar da ake zargi da satar shanu, garkuwa da mutane suka kashe shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Batsari Alhaji Abdulhamid Mamman.
An kashe shugaban jam’iyyar ne a kauyen Sabon garin Dumburawa lokacin da yaje wata hidima da ta shafi rabon gado.
Kamar yadda rahotan ya sanar, maharan sun rutsa da shi ne a garin wanda yake mahaifarsa ce inda suka nemi daukarsa domin yin garkuwa da shi, amma saboda bijirewa wannan bukata yasa har ma ya shige a cikin dakin wani gida hakan yasa maharan suka bi shi kuma suka bude masa wuta lokacin da yake cikin dakin.
- Kauyuka biyu aka kaiwa hari a jihar Katsina
- Dokar hana fita: An kama ababen hawa 307 a jihar Katsina
Maharan sun arce bayan sun yi zaton sun kashe shi kamar yadda majiyar ta ce, amma an dauko shi zuwa babban asibitin garin Batsari inda ba’a dauki wani lokaci ba rai yayi halinsa.
Har ya zuwa rubata wannan rahoton Aminiya tayi kokarin jin ta bakin Kakakin rundunar ‘Yan sanda na Jihar SP Gambo Isa amma abin ya ci tura.
Sai dai wata majiyar ta ce, tabbas jami’an tsaron da aka tura yankin suna iya kokarin su domin wannan shi ne hari na farko da aka kawo a cikin mako daya ko biyu da fara shigar jami’an zuwa yankin na Batsari.
Kazalika, wasu mazauna garin na Batsari da ‘yan kauyukan da ke gab da Batsarin sun ce, suna ganin irin wadannan fulani da ake zargi suna baro cikin daji tare da dabbobin su suna nufo irin wadannan kauyuka na gab da Batsarin.