✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum daya a taron APC a Jigawa

Rikici ya barke a tsakanin kungiyoyin matasan APC a wajen yakin neman zaben.

An kashe wani mutum a wajen gangamin yakin neman zaben jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Kazaure ta Jihar Jigawa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Emmanuel Ekot, ya shaida wa manema labarai cewa, jami’ansa na bin diddigin wanda ake zargi da kisan wanda tuni ya tsere zuwa Jihar Kano.

“’Yan sanda suna bincike a kan lamarin. Wanda ake zargin ya gudu Kano. Rikici ne tsakanin magoya bayan jam’iyya mai aminci da wani dan takara.

“Magoya bayan duk na APC ne. Ba rikici ne tsakanin bangarori biyu ba,” in ji Kwamishinan.

Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Abubakar Badaru, ya jagoranci gangamin yakin neman zaben gwamna na jam’iyyar APC da aka gudanar a garin Kazaure a ranar Talata, inda rikici ya barke tsakanin kungiyoyin matasan magoya bayan jam’iyyar APC da ya yi sanadin mutuwar mutum daya.

Mutumin da aka kashe dai mai goyon bayan dan takarar kujerar Sanatan jam’iyyar ne a shiyyar Jigawa ta Arewa Maso Yamma, Babangida Husseini.

Mazauna garin sun bayyana cewa marigayin Halliru Lafka mazaunin garin Kazaure ne.

Kisan ya haifar da zanga-zanga a tsakanin mazauna garin inda suka rika kona duk wani allo mai dauke da hotunan Husseini.

Masu boren na zarge dan takarar da daukar nauyin ‘yan bangar siyasa wanda ya haifar da tarzoma a garin.

Sai dai Aminiya ta gaza jin ta bakin Hussaini kan lamarin, sakamakon wayarsa na kashe har zuwa lokacin hada wannan rahoto.