✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum biyu a yankin Jama’a

Wadansu mutane da ake zargi ’yan fashi da makami ne sun harbe wadansu mutum uku da ke kan babur a daidai gadar da ta hada…

Wadansu mutane da ake zargi ’yan fashi da makami ne sun harbe wadansu mutum uku da ke kan babur a daidai gadar da ta hada kauyukan Asso da Tanda da ke Masarautar Gwong (Kagoma) a Karamar Hukumar Jama’a da  ke Kudancin Kaduna a ranar Lahadi da daddare.

Yayin da yake yi wa ’yan jarida karin haske kan harin, Shugaban Karamar Hukumar Jama’a, Peter Danjuma Aberik, ya ce ana zargin cewa mutanen da aka harben sun gane maharan nedon haka suka bindige su gudun kada su tona musu asiri, inda nan take daya daga cikin wadanda aka harbe ya mutu.

“Mutum daya ya mutu nan take yayin da ragowar biyun aka wuce da su asibiti bayan samun munanan raunuka inda dayan ya mutu da safiyar Litinin,” inji shi.

Mutanen da aka kashen sun hada da Michael Kure, dan shekara 24 da Emmanuel Thomas, dan shekara 25. “Sai dai an sake ganin gawar wani mutum a gefen hanyar kauyen Wazo, kusa da garin Asso,” inji Shugaban.

Shugaban ya yi kira ga jama’a su kwantar da hankalinsu domin tuni an kai jami’an tsaro kuma gwamnati za ta ci gaba da kokarinta na tsare rayukan jama’a da dukiyoyinsu.

Yayin da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce mutum biyu ne suka rasa rayukansu.

“Da misalin karfe daya na dare ne maharan da ake kyautata zaton ’yan fashi da makami ne suka harbe wadansu mutane da ke haye a kan babur inda nan take daya ya rasa ransa dayan kuma ya cika daga baya yayin da aka garzaya da na ukun zuwa asibiti don kula da shi,” inji shi.