Jami’an tsaro da Kurdawa ke jagoranta da mayakan IS shida ne aka kashe a wani hari da kungiyar IS ta kai kusa da wani gidan yari na masu tsatsauran ra’ayi a Arewacin kasar Siriya.
Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil’adama ta Siriya ta ce, a harin wanda ba a yi nasara ba, an auna wani katafaren ginin tsaron Kurdawa da ke yankin Raqqa ne, wanda ya hada da gidan yarin soji inda ake tsare da wasu mayakan jihadi.
- ’Yan bindiga sun kashe mutum 4 bayan karbar kudin fansa a Taraba
- Mutum 3 sun mutu a hasatrin jirgin sojin Nijar
Jagoran masu sanya ido, Rami Abdel Rahman, ya ce, “Mayakan jihadin sun yi nufin kai hari ne kan gidan yarin sojoji inda ake tsare da muhimman mutane” ciki har da da gawurtattun ’yan ta’adda su 200.
Wannan al’amari ya sanya hukumomin kasar kafa dokar ta baci a Raqa, kana jami’an tsaro na ci gaba da farautar mayakan jihadin da suka samu tserewa.
IS ta dauki hakkin kai harin, inda ta ce wasu biyu daga cikin mayakanta ne suka jagoranci kai harin.