An kashe kimanin mutane biyar a wani rikicin kabilanci da ya samo asali daga gidan giya a Jihar Taraba.
Rikicin gidan giyar ya rikide zuwa na kabilanci tsakanin kabilun Fulani da Tiv a Karamar Hukumar Bali da ke jihar.
Rahotanni na nuni da cewa abin ya samo asali ne sakamakon mutuwar wani bafulatani a wani gidan giya mallakin wani dan kabilar Tiv a yankin Maraban Azagwa da ke Maihula a karamar hukumar.
Shaidu sun ce lamarin ya koma rikici ne bayan dangin Bafulatanin sun zarin dan kabilar Tiv din da kashe musu dan uwa.
- ’Yan kasar Jamus sun raba shanun layya 700 a Kano
- NAJERIYA A YAU: Hadarin Da Ke Tattare Da Cin Naman Layya Fiye Da Kima
Aminiy ta gano cewa an kashe mutane biyar wasu da dama kuma sun samu raunuka a sakamakon rikicin.
Wani mazaunin garin ya bayyana cewa daga bisani kurar ta lafa bayan an tura yan sanda zuwa yankin da abin ya faru.
Kakakin yan sandan Jihar Taraba, DSP kwache Gambo, ta tabbatar da faruwar lamarin amma ta ce rayuka biyu aka rasa, wadanda aka jkkata kuma sauna samun kulawa, amma yanku komai ya lafa.