✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum 5 a rikicin Tibi da Fulani a Nasarawa

Mutum biyar ne aka tabbatar sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka bayan da aka yi taho mu gama tsakanin…

Mutum biyar ne aka tabbatar sun rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka bayan da aka yi taho mu gama tsakanin manoma ‘yan kabilar Tibi da Fulani makiyaya a jihar Nasarawa.

Rikicin ya faru ne a Kadarko a karamar hukumar Keana a jihar Nasarawa da ke kan iyakar jihohin Nasarawa da Benuwe.

Wani rahoto daga bangaren kabilar Tibi ta bayyana cewa, rikicin ya faro ne lokacin da aka yi zargin wani Bafulatani ya yi wa wata mata duka har ta fita a hayyacinta a gonarta.

Majiyar ta kara da cewa, matar ta nemi taimakon makwabcin gonanta wanda shima aka yi zargin Bafulatani ne ya sassare shi da adda a sassan jikinsa.

“Matasa ‘yan kabilar ta Tibi wadanda lamarin ya fusata su ne suka fito daukar fansa wanda hakan yasa suka yi taho mu gama da wasu Fulani wadanda suka gudo daga Udei da ke jihar Benue.

Suma Fulanin sun kai harin daukar fansa a ranar Asabar inda suka kashe mana mata biyu a hanyar su ta zuwa gona” A zargin da majiyar ta kabilar Tibi ya ya wa Fulanin.

A martaninsu, wani dan Kungiyar Miyetti Allah (MACBAN), wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya yi zargin cewa hadin gwiwan matasa ‘yan kabilar Tibi da wasu daga garin Yelwata a jihar Benue sun kashe musu ‘yan uwa guda uku kwanaki uku da suka gabata

Shugaban karamar hukumar Keana, Adamu Adi Giza ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace suna aiki tukuru saboda dakile al’amarin.

Ya ce, “Ina da labarin Fulani biyu da aka kashe sa’annan an fadamin kisan da aka yiwa mata biyu ‘yan kabilar Tibi amma har yanzu ban samu cikakken rahoto akan lamarin ba”.