Akalla mutane 15 ne aka kashe a birnin Shiraz da ke Kudancin Iran, a wani hari da makami da aka kai a wurin ibadar ’yan Shi’a.
Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan harin a cewar Gidan Rediyon Jamus.
Daga bisani dai kungiyar IS mai da’awar jihadi ta dauki alhaki.
Shugaban Addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce za a dauki mataki a kan maharan yayin da ya yi kira ga al’ummar kasar da su ci gaba da kasancewa tsintsiya madauri daya.
A baya dai Hukumomin Iran sun zargi ’yan kasashen waje da kai wannan hari da ya ritsa da mace daya da yara biyu.
Sai dai Shugaban Hukumar shari’a na yankin, Kazem Moussavi, ya ce an kama mutum daya daga cikin wadanda suka kai harin.
Dama dai a farkon watan Afrilu, wani matashi dan asalin kasar Uzbekistan ya daba wa wasu malaman Shi’a biyu wuka har lahira, tare da raunata na uku a harabar hubbaren Imam Reza da ke Mashhad, birni na biyu mafi girma a Iran.
Amma an rataye maharin tun watanni hudun da suka gabata bayan da aka same shi da laifin da aka tuhume shi da aikatawa.