Akalla mutane 134 ne suka riga mu gidan gaskiya a cikin kwanaki biyar sakamakon hare-haren da aka kai wasu kananan hukumomi uku na Jihar Benuwe.
A karshen wannan makon ne Gwamna Samuel Ortom ya bayyana cewa, wadanda lamarin ya rutsa da su an kashe su ne a kauyuka daban-daban a kananan hukumomin Otukpo, Apa da Guma.
- Ramadan: Masu karamin karfi 750 sun sami tallafin abincin azumi a Kano
- Yadda dan Najeriya ya bata wa Real Madrid ruwa a La Liga
Wakilinmu ya ruwaito cewa, adadin wadanda suka mutu a harin na ranar Laraba 5 ga watan Afrilu da aka kai kauyen Umogidi da ke Karamar Hukumar Otukpo, ya karu zuwa 52, bayan samun mamata 46 a farko.
Bayanai sun ce an kashe wasu mutane uku a kauyen kwana guda gabanin kisan gillar da aka yi.
Haka kuma, adadin wadanda suka mutu a sansanin ‘yan gudun hijira na Ngban da ke Guma a daren Juma’a, 7 ga watan Afrilu, ya karu daga 36 zuwa 38, yayin da wasu sassan Karamar Hukumar Guma suka sami mamatan da ba a tantance adadinsu ba, duk a hare-haren da ‘yan bindigar suka kai a cikin kwanaki biyar.
Hakazalika, a Karamar Hukumar Apa, an ce an kashe mutane 47 a ranar Litinin 3 ga Afrilu, a kauyuka daban-daban ciki har da al’ummar Ikobi inda aka kashe wani basarake tare da wasu jama’arsa.
Ortom ya bayyana cewa an kashe jimillar mutane 134 a cikin kasa da mako guda yayin da yake zantawa da manema labarai lokacin da ya ziyarci sama da mutane 36 da suka jikkata — akasari mata da kananan yara — a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Benue (BSUTH).
Da yake kira ga al’umma da shugabanninsu da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda, ya kuma bukaci su ci gaba da kasancewa masu taka-tsan-tsan a kowane lokaci domin a samu nasarar fatattakar maharan.
Gwamnan ya nanata kiransa ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan kada ya tsaya iya magana ta fatar baki wajen yin Allah wadai, yana mai neman da ya tura karin sojoji domin dakile aukuwar wadannan kashe-kashe.
A bayan nan ne Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da kashe-kashen da aka samu a Jihar Benuwe da ke Arewa maso Tsakiyar Najeriya.
A wata sanarawa da mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu ya fitar, Buhari ya ce za a yi duk mai yiyuwa wajen kawo karshen tashe-tashen hankula a kasar.
Buhari ya yi Allah-wadai kan amfani da abin da ya kira ta’addanci wajen rura wutar fadan kabilanci a kasar.
Ya kuma bayar da umarnin zakulo maharan domin fuskantar hukunci kan laifin da suka aikata.
Shugaban ya kuma jajanta wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon harin.
“Muna mka sakon ta’aziyyarmu ga iyalan wadanda aka kashe. Kuma kasarmu za ta tsaya tsayin-daka domin yakar ayyukan bata-gari da na ’yan ta’adda,” in ji Buhari.
Daga karshe shugaban ya umarci jami’an tsaron kasar da su kara sanya idanu tare da sake nazarin fannin tsaro musamman a yankunan da lamarin ya faru.