✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe matashi a Delta saboda murnar nasarar Buhari a kotu

A makon jiya ne wani matashi mai suna Elvis Omoiri ya gamu da ajalinsa sakamakon murnar nasarar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya samu a…

A makon jiya ne wani matashi mai suna Elvis Omoiri ya gamu da ajalinsa sakamakon murnar nasarar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya samu a shari’ar zabe da jam’iyyarsa ta APC ta yi tare da dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar.

Kamar yadda Aminiya ta samu rahoto hakan ya faru ne a wata mahada da ke Okolona, a Karamar Hukumar Warri ta Yamma lokacin da Omoiri,  ya je shagon sayar da barasa  ranar Alhamis kwana daya da yanke hukuncin Kotun Karar Zaben Shugaban Kasa inda matashin da abokansa suna cikin holewa suna murnar nasarar da Buhari ya samu sai mai shagon Uduophori  wanda dan ga-ni-kashe-nin PDP ne ya daba wa Elvis kwalba wanda nan take  ya rasu aka kai shi asibiti daga bisani likitoci suka tabbatar da rasuwarsa.

Wani wanda al’amarin ya faru yana wurin da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa wakilin Aminiya cewa, “Ana cikin shagulgulan murnar nasarar ce mai shagon ya dauko kwalba ya buga wa Elvis Omoiri, saboda bambancin ra’ayinsiyasa.”

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Obie Omo-Agege ya yi tir da kisan inda ya bayyana kisan da aka yi wa mai goyon bayan Jam’iyyar APC din da “tsabar dabbanci da rashin sanin ya kamata.” A sanarwar da Kakakin Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan, Mist aYomi Odunuga ya fitar, ya ce Sanata Omo-Agege  ya bukaci a gudanar da bincike kan wannan danyen aiki da aka yi.