✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe masu garkuwa da mutane da kuɓutar da wasu

Cikin nasarorin jami'an tsaron an ceto mutanen da aka sace, da kashe wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da kuma ƙwato manyan…

Hukumomin ’yan sandan Najeriya tare da haɗin gwiwar wasu hukumomin tsaro sun samu gagarumar nasara a ƙoƙarin da suke na daƙile munanan laifuka a ƙasar.

Na baya-bayan nan dai shi ne ceto mutanen da aka sace, da kashe wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da kuma ƙwato manyan bindigogi da alburusai a jihohin Delta da Katsina.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ya ce a jihar Katsina an samu gagarumar nasara a ranar 8 ga watan Yunin 2025, inda haɗin gwiwar JTF da suka haɗa da jami’an ’yan sanda da sauran jami’an tsaro suka daƙile wani yunƙurin yin garkuwa da mutane a hanyar ƙauyen Danmusa  zuwa  Mara Dangeza a ƙaramar hukumar Danmusa.

Adejobi ya ce hakan na iya yiwuwa ne ta hanyar shigar da wasu gungun ’yan bindiga da suka yi yunƙurin guduwa da waɗanda aka yi garkuwa da su a wani artabu da ya kai ga ceto mutum 11.

Nasarar da aka samu yankin Kudu maso Kudu

A halin da ake ciki kuma, a yankin Kudu maso Kudu, Jihar Delta, hukumar ’yan sanda ta kama wani Abubakar Hassan, wanda babban wanda ake zargi da aikata laifin satar mutane ne a tsakanin jihohin Delta da Ribas da Imo, da Enugu.

Jami’an da ke da alaƙa da samun nasarar sun yi hakan ne yayin da suke aiki da sahihan bayanai.

A yayin da ake yi masa tambayoyi, Hassan ya bayyana cewa shi ne ya jagoranci gudanar da hari a yankin Ughelli-Ozoro na jihar mai arzikin man fetur.

Ya kuma jagoranci jami’an ’yan sanda zuwa maɓoyarsa a wani daji da ke Ozoro. A can jami’an sun ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu da tarin alburusai huɗu da harsashi guda talatin da biyu.