✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe masu faskare 5, an sace wasu 10 a Binuwai

Akwai kuma mutum 10 da ba a gan su ba

Akalla gawa masu faskare biyar aka tsinta a harin da wasu da ba a kai ga gano su wane ne ba suka kai Karamar Hukumar Guma da ke Jihar Binuwai.

Aminiya ta gano cewa mutane 10 ne kuma ake zargin sun bata, kuma tuni an baza komar masu nemo su a dajin garin.

Shugaban Karamar Hukumar, Caleb Aba ya shaida wa wakilinmu cewa lamarin ya faru ne da yammacin Litinin a kauyen Mbagwen, sai dai ba a sanar da shi ba a kan lokaci sai ranar Talata.

Aba ya ce dillalan itace ne lamarin ya rutsa da su a ranar Litinin, lokacin suka je kwashe itacen da suka saro a dajin Mbagwen da ke wani kauye a kusa da Yelewata a Guma.

“Masu faskaren su 15 sun gama zuba icen a mota sun dau hanyar komawa gida aka far musu,” inji Aba.

“Yanzu dai mutane biyar ne suka mutu sai kuma 10 da ba a san inda suke ba, ba mu san ko kashe su aka yi ko sace su ba, amma dai mun baza mutane su binciko su a daji,” a cewar Shugaban Karamar Hukumar.

Jami’ar Hulda da jama’a ta Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta Binuwai, SP Catherine Anene ta ce ba ta da labarin aukuwar lamarin, domin tana wurin wani taron bita a wajen Jihar.