Rundunar ‘Yan Sandan jihar Edo ta kama wasu mutum uku a wani dakin tsafi dauke da tsofaffin gawarwaki 20 da aka busar.
Rundunar ta bayyana hakan ne ranar Alhamis a Benin, babban birnin jihar cikin wata sanarwa da ta fitar ta bakin mataimakin Kakakinta, ASP Jennifer Iwegbu.
- Ma’aikata sun yi barazanar rufe ilahirin makabartun Abuja
- Harin bom ya kashe mutum 21 a masallaci a Afghanistan
Jennifer ta ce an gano gawarwakin ne a wani gida da ke unguwar Asoro da ke birnin na Benin.
Ta ce, “Biyo bayan wasu bayanan sirri da muka samu cewa an gano wasu gawarwaki a unguwar Asoro, mun tura tawagarmu cikin gaggawa unguwar, kuma mun samu nasarar kamo mutane uku a gidan, yayin da sauran suka tsere.
“Baya ga haka kuma, mun gano gawarwakin maza 15 da su ma aka busar, da na mata uku, sai kuma na kananan yara biyu.
“Ganin haka Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, Abutu Yaro, ya ba wa Mataimakinsa na sashin binciken sirri umarnin binciko musabbabin mutuwar gawarwakin,” inji ta.
Jennifer ta kuma ce al’ummar jihar su kwantar da hankalinsu, domin za su cigaba da tabbatar da sun kiyaye rayuka da dukiyoyin su kamar dai yadda doka ta dora musu.