✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe malamai 10, an sace 50 a wata 10 a Kaduna

’Yan bindiga sun kashe malaman makaranta 10 sun kuma sace wasu 50 a cikin wata 10 a Jihar Kaduna.

’Yan bindiga sun kashe malaman makarantu 10, wasu 50 kuma na hannunsu a  Jihar Kaduna, daga watan Janairu zuwa Oktoban 2022.

Kungiyar Malaman Sakandare da Firamare ta Kasa (ASUSS), Reshen Jihar Kaduna ta ce hakan ta faru da malaman makarantun ne a a kananan hukumomin Kachia, Chikun, Kagarko, Sanga da kuma Kaura a jihar.

Shugaban ASUSS a jihar, Kwamred Ishaya Dauda, ya ce, “Matsalar rashin tsaro ta fi ritsawa da malaman sakandare, inda daga watan Janairu zuwa Oktoban 2022 da muke ciki, an kashe malamai sama da 10 wasu 50 kuma har yanzu suna hannun masu garkuwa da mutane. Dalibai da dama ma an yi garkuwa da su.”

A jawabinsa na Ranar Malamai ta Duniya ta 2022, Kwamred Ishaya Dauda ya yi kira ga jami’an tsaro da su yi mai yiwuwa wajen ceto malaman da ke hannun masu garkuwa da mutane.

Ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kaduna bisa hadin gwiwarta da ’yan banga wajen samar da tsaro a makarantu da ke jihar.

“An girke ’yan banga akalla shida a kowace kamaranta da ke fadin jihar domin samar da tsaro da aminci ga malamai da dalibai.”

Daga nan sai ya yi kira ga gwamnatin da ta bullo da shirye-shiryen da za su rage radadin hauhawar farashin kayan masarufi da kuma biyan hakkokin wadadna suka yi ritaya domin saukaka musu.