✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe makiyayi a hanyarsa ta dawowa daga kiwo a Kudancin Kaduna

A yammacin ranar Litinin ne wasu gungun mutane suka farwa wasu yara makiyaya bayan sun taso daga kiwo a kan hanyarsu ta dawowa gida inda…

A yammacin ranar Litinin ne wasu gungun mutane suka farwa wasu yara makiyaya bayan sun taso daga kiwo a kan hanyarsu ta dawowa gida inda suka kashe wani matashi mai kimanin shekara 15 mai suna Abdulkadir Umar.

Lamarin ya faru ne a gundumar Kukum da ke yankin Kagoro, wajen da ya yi kaurin suna kan rikicin manoma da makiyaya a Karamar hukumar Kaura da ke jihar Kaduna.

Yayin da yake yi wa Aminiya karin haske, shugaban al’ummar Fulanin masarautar Kagoro kuma Ardon Fada, Alhaji Isa Ori ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe biyar na yamma bayan yaran sun taso daga kiwo suna hanyar dawowa gida inda mutanen yankin suka taso musu abin da yasa yaran suka firgita suka tsere don tsira da rayukansu.

“Sai dai bamu ga daya yaron ya dawo gida ba abin da yasa aka kira jami’an tsaro aka bazama nemansa washegari, inda aka tsinci gawarsa a gefen wani rafi jini na fita ta hancinsa, da alamar an murde shi ne da karfin tsiya ba wai sun yi amfani da wani makami bane don kada a gane.” In ji shi.

Ya ce, sun yi jana’izar yaron a ranar Talata da yamma bayan sun yi masa sutura inda aka birne shi a makabartar garin Manchok da ke karamar hukumar.

“A yanzu haka da nake magana da kai mun kammala jana’izar kenan kuma shugaban karamar hukumar da kansa tare da rakiyar sakatarensa da wakilin DPO na karamar hukumar duka sun halarci jana’izar.”

Shugaban kungiyar Fulani makiyaya ta kasa ta Miyetti Allah reshen karamar hukumar Kaura Alhaji Salisu Ibrahim Hari, wanda shi ma ya halarci jana’izar ya shaidawa Aminiya ta wayar tarho cewa, babban abin takaici ne musamman a daidai wannan lokaci da ba a dade da shiga sabuwar shekara ba, a tare kananan yara ba tare da sun aikata laifin komai ba a hau su da bugu a murde karamin yaro har a xauki ransa, sai dai ya yi kira ga ‘yan uwansa makiyaya da su kwantar da hankalinsu su ci gaba da bin doka da oda kamar yadda aka san su da shi kuma su jira hukuma tayi aikinta domin jami’an tsaro na ci gaba da bincike kan lamarin.

Yayin da yake tabbatarwa da Aminiya faruwar lamarin, shugaban karamar hukumar Kaura Dakta Bege Katuka Ayuba, ya yi kira ga jama’ar yankin da su kai hankalinsu nesa.

Katuka, wanda ya halarci jana’izar Bafulatanin ya ce ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen lalubo wadanda suka aikata hakan.

“Ka san an same shine a bakin rafi. Yanzu muna jiran binciken likita ne don tabbatar da cewa, kashe shi aka yi ko kuwa ya fada ruwa ne garin gudun ceton rai, amma zamu hukunta duk wadanda suka aikata hakan.” In ji shi.

Duk wani yunkuri na jin ta bakin Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna DSP Yakubu, ya citura domin lambarsa ba ta shiga a lokacin hada wannan rahoton sannan bai amsa sakon karta kwana da aka tura masa ta waya ba.