✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe magoya bayan Real Madrid

Wasu ’yan bindiga dadi da ake kyautata zaton ’yan kungiyar ISIS ne da ke Iraki sun yi wa magoya bayan kulob din Real Madrid mazauna…

Wasu ’yan bindiga dadi da ake kyautata zaton ’yan kungiyar ISIS ne da ke Iraki sun yi wa magoya bayan kulob din Real Madrid mazauna Iraki kwanton bauna kuma suka kashe akalla 12 daga cikinsu, yayin da wasu kuma suka samu raunuka. Wannan shi ne hari na biyu da ake kai wa magoya bayan a tsakanin makonni biyu a Iraki.
Rahotannin da ke fitowa sun nuna al’amarin ya faru ne a ranar Asabar da ta gabata a lokacin da magoya bayan suke kallon yadda wasa ke gudana a tsakanin kulob din Real Madrid da na Atletico Madrid a wasan karshe na gasar zakarun kulob na Turai (Champions League).  An ce ana gab da tashi wasan ne sai kawai maharan suka budewa magoya bayan kulob din wuta a wani gidan kallon kwallo al’amarin da ta sa aka yi mummunan asarar rayuka yayin da wadansu da dama kuma suka samu munanan raunuka.
Kafar sadarwar The Telegraph da ke Ingila ta kalato cewa, wadansu mahara su kimanin 4 ne suka yi wa gidan kallon kwallon kawanya dauke da muggan makamai kuma suka bude musu wuta a yayin da suke kallon kwallo a garin Bakuba da ke da nisan mil 40 daga babban birnin kasar, Bagdad.
Shugaban kungiyar magoya bayan kulob din Madrid a Iraki Ziad Albidami a wata hira da ya yi da manema labarai ya ce al’amarin ya faru ne ana gab da tashi daga wasan.  Ya ce mutum 12 ne suka rasu yayin da 8 kuma suka samu mummunan raunuka kafin a garzaya da su asibiti.
Ya ce dukkan wadanda al’amarin ya rutsa da su matasa ne da shekarunsu ya kama daga 18 zuwa 30.  Kuma dukkansu ana kyautata zaton ’yan asalin Iraki ne.
Kimanin makwanni biyu da suka wuce ma wasu ’yan bindiga suka bude wuta a hedkwatar kungiyar magoya bayan kulob din Real Madrid da ke garin Balad kusa da Bakaba inda suka kashe mutane da dama.  Sannan a ranar 13 ga watan Mayun 2016 ma wadansu ’yan bindiga sun bude wa magoya bayan Madrid wuta inda suka kashe akalla mutane 16 a wani gidan cin abinci da ke Al-Furat a Iraki kuma fiye da mutum 20 suka jikkata.
kungiyar ISIS dai ta dauki nauyin dukkan wadannan hare-hare da ta kai wa magoya bayan kulob din Real Madrid sai dai ba ta bayyana dalilinta na yin haka ba.