✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe Magidanci da sace matarsa da wasu 2 a jihar Kogi

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe wani Magidanci mai suna Alhaji Nuhu Yusuf, sannan suka yi garkuwa da…

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe wani Magidanci mai suna Alhaji Nuhu Yusuf, sannan suka yi garkuwa da matarsa mai suna Ramatu Nuhu tare da wasu mutum biyu a kauyen Aseni da ke Karamar Hukumar Kotonkarfe jihar Kogi.

Kauyen Aseni, yana babbar hanyar Abuja zuwa Lokoja kimanin nisan kilomita 9 daga garin Abaji iyaka da babban birnin tarayya Abuja.

Wani mazaunin unguwar Aseri, mai suna Attahiru Salihu, ya ce ‘yan bindigar sun shiga kauyen ne da misalin karfe 2 na tsakar dare inda suka yi ta harbi daga lungunan kauyen.