✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe limamin coci a Katsina

Yan bindigar sun kashe limamin ne a Karamar Hukumar Malumfashi a Jihar Katsina.

Wasu ’Yan bindiga da ba a san daga inda suka fito ba sun harbe wani Limamin Cocin Katolika mai suna Rabaran Fr Alphonsus Bello.

’Yan bindigar sun kashe limamin ne a wani harin da suka kai cocinsa na St.Vincent Ferrer Catholic Church da ke Karamar Hukumar Malumfashi a Jihar Katsina.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, ’Yan bindigar sun kai hari cocin ne da misalin karfe 11 na daren Alhamis.

Kamar yadda wasu daga cikin wadanda suka shaida faruwar lamarin suka ce, ’yan bindigar na shiga cikin cocin sai suka tunkari inda limamin ya ke kuma suka ci gaba da harbe-harbe har suka tafi da shi.

Majiyar ta shaida wa Aminiya cewa, Limamin da aka kashe ya yi wa ’yan bindigar tirjiya ne a lokacin da suke yunkurin yin awon gaba da shi, inda daga bisani suka samu nasara a kansa duba da yadda masu iya magana kan ce sarkin yawa ya fi sarkin karfi.

Bayan ’yan bindigar da ba a tantace adadinsu ba sun yi awon gaba da Rabaran Alphonsus, kwatsam sai gawarsa aka tsinta da safiyar yau Juma’a yashe a gefen hanya.