An tsinci gawar wata budurwa mai suna Mojisola Awesu dalibar Kwalejin Fasaha ta Jihar Kwara.
Budurwar mai shekara 21 da aka bayyana ɓacewarta tun ranar 9 ga watan Agustan 2024, an same ta babu rai a wani wajen zubar da shara da ke unguwar Aleniboro a Ilorin, babban birnin jihar.
- Gwamnan Filato ya dakatar da Kwamishinoninsa 2
- Zulum ya raba wa magidanta 10,000 kayan abinci da 150m a Borno
Rundunar ‘yan sandan jihar, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata.
Kakakin rundunar, DSP Toun Ejire-Adeyemi, ya bayyana cewa marigayiyar ta samu kiran waya daga wata Mis Timileyin a ranar 9 ga watan Agusta, 2024, game da wani taron da ɗaliban makarantar a Offa, da suka shirya.
Matar ta gabatar da marigayiyar ga wani Mista Adebayo Happiness, ɗaliban Jami’ar Summit, wanda ake zargin ya gayyace ta zuwa liyafar dare a kan zargin cewa ta yi a matsayin budurwarsa kan kudi Naira 15,000.
“Duk da haka, marigayiya Mojisola ta sanarwa da abokiyar zamanta, wata Blessing O, cewa ta ji ba dadi a otal din da Adebayo Happiness ya sauke ta kuma ta lura cewa babu wani biki a wajen da aka ce.
“Ba daɗewa bayan wannan tattaunawar wayarta a kashe ta kuma duk ƙoƙarin da Miss Blessing ta yi na samunta bai yi nasara ba”, in ji shi.
Ta ce an kama wanda zargin da aikata kisan kuma an miƙa shi ga cibiyar binciken laifuka ta jihar.