Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a ranar Talata ya jagoranci bikin karrama sha’iran da suka zama zakaru a gasar musabakar yabon Annabi Muhammad (S.A.W) irinta ta farko a Jihar.
Kungiyar Raudhatul Rasul Ayagi ce ta shirya gasar wacce ta tattaro sha’irai daga fadin Jihar kuma suka fafata a musabakar wacce aka yi wa lakabi da ‘Dausayin Bege’.
Gasar dai ta mayar da hankali ne akan kyawawan dabi’un Ma’aiki, musamman a wajen hakuri.
Wadanda suka sami nasara a musabakar sun hada da Nafisa Usman Abdullahi, wacce ta zo ta daya, sai Sa’adatu Sani da ta zo ta biyu, yayin da Abubakar Nuhu Salis ya zo na uku.
Tun farko da yake jawabi, Shugaban Kungiyar ta Raudhatul Rasul, Malam Bilyaminu Zakariyya ya ce sun shirya gasar ne da nufin kara jefa soyayyar Annabi (S.A.W) musamman a zukatan kananan yara.
“Wannan shi ne karo na farko da muke shirya irin wannan gasa, kuma sha’irai da dama sun fafata, amma daga ciki, alkalan gasa suka tantance guda 12 wadanda su ne suka cika ka’ida.
“Daga cikinsu, yau muna bikin karrama wadanda suka yi na daya da na biyu da na uku,” inji shi.
Da yake nasa jawabin, Mai Martaba Sarki yaba wa wadanda suka shirya gasar ya yi, inda ya yi kira ga sauran jama’a da su dage wajen kafa irin wadannan kungiyoyin da za su kara wa mutane soyayyar Ma’aiki.
Yayin bikin dai, an ba wadanda suka yi nasarar takardar shaidar zama zakaru da kyauta kudi N200,000 ga wacce ta zo ta daya, N100,000 ga ta biyu, sai N50,000 ga wanda ya zo na uku.