✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An karrama Bello BMB da Ahmad Mai Shanawa a Jos

Wata kungiya mai suna Young Media Forum International mai hedikwata a kasar Ghana da kuma rassa a kasashen Najeriya da Nijar da kuma Kamaru ta…

Wata kungiya mai suna Young Media Forum International mai hedikwata a kasar Ghana da kuma rassa a kasashen Najeriya da Nijar da kuma Kamaru ta karrama fitaccen jarumi Bello Muhammad Bello a garin Jos a ranar Lahadin da ta gabata.

kungiyar ta kuma karrama fitaccen mawaki Ahmad Mai Shanawa bisa amfani da yake yi da wakokinsa wajen fadakarwa da nishadantarwa da kuma ilimantarwa. 

An gabatar da bikin karramawar ne da Lambu Chinese Garden da ke birnin Jos, inda ya samu halartar ’yan fim da ’yan siyasa da ’yan kasuwa da ’yan jarida da kuma sauran jama’a da ke ciki da wajen Jihar Filato.

A lokacin da yake jawabi shugaban kungiyar na duniya, Abdulkarim Mostafa wanda dan kasar Ghana ne ya ce jarumin Bello BMB ya cancanci karramawar bisa rawar da yake takawa wajen ganin masana’antar fina-finan ta bunkasa.

Ya ce, “Jarumin ya kasance kamar wata fitala da ke haskaka masana’antar fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood. BMB yana taka rawa sosai wajen fadakarwa da nishadantarwa da kuma ilimantar da al’umma ta hanyar fina-finan da yake shiryawa ko bada umarni ko kuma fitowa a ciki. 

Ya kara da cewa sannan tallar fina-finai da yake yi musamman da Turanci tana kara sanya wadanda bas a jin Hausa son fina-finan Hausa.

“Wannan rawa da yake takawa ta sanya muka karrama shi, inda muke fatan zai bada kaimi donci gaba da bada gudunmuwar da yake,” inji shi.

Ya ce, dangane da Ahmad Shanawa kuwa wakokinsa da suka hada da ‘Cakwai’ da ‘Ashe Gaskiya Tana da Dadi’ da kuma ‘kamas’ sun kasance daga cikin wakokin da suke tashe a Najeriya da kuma kasashe irinsu Ghana da Nijar da kuma Kamaru, har ma da sauran kasashen duniya

“A lokacin da na ziyarci kasar Afirka da Kudu na hadu da mutane ba ma ’yan Afirka ba da suka karbi wakar ‘Cakwai’ a wurina, kuma sun ji dadinta sosai. Hakan ya sanya muka karrama shi.” 

A lokacin da yake jawabi Bello Muhammad Bekllo wanda ake masa lakabi da ‘Cibilian General ya gode wa kungiyar bisa ga karramawar da suka yi masa.

“Na gode wa Allah bisa ga wannan karramawar da aka yi mini, hakan ya nuna mini duk wanda ya kaskantar da kansa a wurin Ubangiji (SWT) to zai samu daukaka da kuma yarda a wurin mutane,

“Na samu wannan karramawar ne saboda fandeshin da na gina ayyukana a kai, idan ka yi aikin kwarai duniya ta amfana, to kai ma za ka ga amfanin hakan a gare ka. Samun wannan nasarar ba hadari ba ne, ayyukan da na yi ne suka kawo hakan, inda a lokacin da nake ayyukan na jajirce, na tsayar da gaskiya da kuma yi amfani da fikira da basira da kuma dabara kafin na kai ga yinsu, kuma Allah ne Ya hore mini hakan.”

Ya ce, ya sadaukar da karramawar ga ’ya’yansa ’yan biyu da matarsa da kuma masoyansa da suke ba shi goyon baya ba dare ba kuma rana.

Shi kuwa mawaki Ahmad Shanawa ya mika godiyarsa ga Allah bisa ga karramawar, sannan ya sadaukar da karramawar ga masoyansa.