Masarautar Atyap da ke Karamar Hukumar Zangon Kataf a Jihar Kaduna, ta karrama Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa.
An karrama Babban Hafsan Tsaron ne da sarautar Tsuwong Atyao wato Ginshikin Katafawa.
- Dalilin da LP za ta zama babbar jam’iyyar adawa a bana — Peter Obi
- Ronaldo ne dan wasa mafi zura kwallaye a 2023 — IFFHS
Sarkin Atyap, Dominic Gambo Yahaya ya ce masarautar ta fuskanci kalubalen rashin tsaro a shekarar da ta gabata, inda ta rasa rayukan mutane da dukiyoyi masu yawa.
Da yake bayani a wajen nadin sarautar a Fadar Sarkin Atyap da ke Atek Njei, Sarki Gambo ya yi fatan kada Allah ya maimaita musu irin haka a sabuwar shekarar 2024.
Sarkin ya yaba wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu da ya zabi dan kabilarsu laakari da cancantarsa wajen danka masa ragamar babban hafsan tsaron kasa.
Haka kuma, Sarki Gambo ya yi kira ga gwamnati da ta samar da abubuwan more rayuwa a masarautar.
A nasa jawabin, Janar Christopher Musa ya ce bayan amsar sarautar da hannu biyu, zai yi iyaka kokarinsa don ganin ba a sake samun matsalar tsaro a masarautar Atyap da ma Karamar Hukumar Zangon Kataf da kuma Najeriya baki daya.
Janar Musa ya kuma yi kira ga matasa da su yi watsi da harkar banza su rungumi hanyar da za ta fisshe su don samun mafita a rayuwa.
Shugaban taron, Alhaji Abubakar Mustafa (Iyan Gubuci) wanda ya bayyana dadaddiyar alakar da ke tsakaninsa da Sarkin Atyap, ya roki mutanen yankin da su yi kokari wajen dawo da kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu.
Aminiya ta ruwaito cewa, makadan gargajiya na kabilar Katafawa da na Chawai da masu rawar koroso da masu busa kaho sun nishadantar da mahalarta taron.
Taron ya samu hakartar kabilun Hausawa da Katafawa da Fulani tare da manyan baki da suka hada da Sarakunan Jama’a da Attakar da Chawai da Kagoma da Fantswam da na Chikun da Kufana da Kachia da Dnata da Kudaru da Ikulu da Wakilan sarakunan Piriga da na Anghan da na Marwa da kuma na Barde.