Gwamnatin Tarayya ta sake kara wa’adin hada layukan waya da Lambar Shaidar Zama Dan Kasa ta NIN zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2021.
Karin wa’adin ya biyo bayan wani taro da Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami ya jagoranta ta bidiyo wanda kuma ya samu halartar shugaban Hukumar Sadarwa (NCC), Farfesa Umar Garba Danbatta da takwaransa na Hukumar Kula da Shaidar Zama dan Kasa (NIMC), Farfesa Adeolu Akande.
- Sun canza gida sau 18 a shekara uku saboda tsoron kyankyaso
- Biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane haramun ne —Farfesa Maqari
- Boko Haram ta kashe mutum 30 ta tashi sansanin soji a Borno
Masu magana da yawun Ma’aikatatun Sadarwa da NCC, Ikechukwu Adinde da Kayode Adegoke ne suka sanar da hakan a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka fitar ranar Talata.
Sun ce karin wa’adin ya biyo bayan bukatar da bangarorin masu ruwa da tsaki a lamarin suka nema cewa yin hakan zai ba su damar yi wa dukkan ’yan kasa yin rijistar.
“Mun samu gagarumin cigaba a aikin hada NIN da layukan waya. Sama da ’yan Najeriya miliyan 54 ne suka yi rijistar ya zuwa yanzu, wanda hakan ke nufin kusan masu amfani da layukan waya miliyan 190 ke nan, tun da bincike ya nuna kusan kowane mai lambar NIN na da layuka uku zuwa hudu.
“Tsarin da muka jima muna nema na manhajar Android da zai taimaka wajen sanya aikin ya yi sauri shi ma yanzu ya kammala,” inji sanarwar.
Bugu da kari, sanarwar ta ce kamfanonin sadarwa sun bude wuraren yin rijistar da dama a fadin kasa domin saukaka wa mutane yin rijistar.
Sassa na 27 da na 29 na NIMC na 2007 ya wajabta wa ’yan kasa yin amfani da lambar NIN wajen cin gajiyar shirye-shiryen gwamnati da dama.