✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya tsawaita lokacin ritayar malaman makarantu da shekara 5

An yi wa malaman makarantun gwamnati karin shekara biyar a shekarunsu na aiki kafin a yi musu ritaya daga aiki a Najeriya. Daga yanzu za…

An yi wa malaman makarantun gwamnati karin shekara biyar a shekarunsu na aiki kafin a yi musu ritaya daga aiki a Najeriya.

Daga yanzu za a koma yi wa malamai ritaya ne bayan sun cika shekara 65 da haihuwa ko kuma idan suka cika shekara 40 suna aikin koyarwa.

Da yake sanar da hakan, Hadimin Shugaban Kasa kan Kafofin Sada Zumunta, Bashir Ahmad, ya ce, “An yi wa malaman makarantu a fadin Najeriya karin shekarun aiki da shekara biyar bayan da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan dokar Hadaddden Tsarin Shekarun Riytayar Malamai ta Najeriya.”

Hakan na nufin an kara lokacin yin ritayar malaman makarantu daga shekara 60 zuwa shekara 65 da haihuwa, ko kuma shekara 40 a aikin koyarwa.

Malaman sun samu karin shekarun aikin ne bayan rattaba hannu da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kan sabuwar dokar Hadaddden Tsarin Shekarun Riytayar Malamai ta Najeriya.