✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kara lokacin rajistar N-Power

An kara lokacin domin ba wa karin matasa damar shiga rukuni na uku.

Gwamnatin Tarayya ta tsawaita wa’adin kammala rajistar matasa masu nema shiga shirin aikin tallafi na N-Power, rukuni na uku.

Ministar Jinkai da Kyuatata Rayuwa, Sadiya Umar Faruq ta wallafa a shafinta na Twitter cewa an “kara lokacin rufe shafin rajistar zuwa ranar 8 ga Agusta, 2020”, sabanin 26 ga watan Yuli da aka sanar da farko.

Mataimakiyar Daraktan Yada Labaran ma’aikatar, Rhoda Ishaku, ta ce hakan za ba wa karin matasan da suka cancantta damar yin rajista, duba da matsalar da wasunsu suka samu wajen yin rajistar ta intanet.

“Kara lokacin ya zama dole domin bayar da cikakkar dama ga dukkan masu bukatar shiga shirin”, wanda ta ce matasa miliyan biyar sun yi rajista suna neman a dauke su.

A baya ma’aikatar ta ce za ta rufe rajistar shiga N-Power karo na ukun ne a ranar Lahadi 26 ga Yuli, inda daga bisani za a dauki matasa 400,000 daga cikinsu aikin.

Idan ba a manta ba, a baya rahotanni sun bayyana yadda wasu daga cikin matasan da ke neman shiga shirin suka yi ta samun matsala wajen shiga shafin a intantet.

A makon jiya matasa 500,000 na rukunin farko da na biya na shirin sun gudanar da zanga-zanga a Abuja, inda suke bukatar Gwamnatin Tarayya ta biya kowannensu kudin sallama Naira 600,000 sannan ta dauke su aiki.

Amma sakon da ta wallafa Twitter ministar ta ce yaye rukunin farkon da na biyun “ba don wahalarwa ba ne, sai don su bayar da wuri ‘yan uwansu ma su samu damar cin gajiyar shirin”.