✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kara farashin man fetur zuwa N143.80

Gwamnatin Tarayya ta sanar da kara farashin man fetur zuwa N143.80 a kan kowacce lita. Hukumar Kayyade Farashin Mai ta Kasa (PPPRA) ta bayyana haka…

Gwamnatin Tarayya ta sanar da kara farashin man fetur zuwa N143.80 a kan kowacce lita.

Hukumar Kayyade Farashin Mai ta Kasa (PPPRA) ta bayyana haka a wata sanarwa a ranar Laraba.

Sanarwar da aka raba wa dillalan mai dauke da kwanan watan daya ga watan Yuli ta ce, “Bayan la’akari da yanayin kasuwar mai a watan da ya gabata da kuma nazarin halin da dillalai suke ciki, muna bayar da shawarar a kara farashin mai zuwa tsakanin N140.80 da N143.80 daga farkon watan Yulin 2020.

“Mun umarci dukkan dillalai da su sayar da man a tsakanin wadannan farashin kamar yadda PPPRA ta ba da shawara.

Kusan sau uku hukumar tana rage farashin man a bana sakamakon faduwarsa a kasuwar duniya, ko da yake wannan ne karon farko da aka kara kudinsa a shekarar da muke ciki.