✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kara farashin kananzir zuwa Naira 83

A farkon makon nan ne Hukumar da ke Kula da kayyade Farashin Albarkatun Man Fetur (PPPRA) ta sanar da kari a farashin kananzir  daga Naira…

A farkon makon nan ne Hukumar da ke Kula da kayyade Farashin Albarkatun Man Fetur (PPPRA) ta sanar da kari a farashin kananzir  daga Naira 50 zuwa Naira 83 kowacce lita.
Sanarwar da hukumar  ta fitar ta ce gidajen mai na gwamnati mallakar NNPC ne kawai za su dinga sayar da shi a wannan sabon farashin, kamar yadda BBC ta bayyana.
Hakan na cikin matakan da gwamnati ta xauka na janye tallafin da take bayarwa a kananzir da ma wasu albarkatun man fetur a kasar nan.
Sanarwar ta nuna cewa gwamnati za ta samu ribar fiye da Naira 10 a kan kowacce litar kananzir a wannan sabon farashin.
Masana sun nuna cewa wannan sabon farashin ba zai yi matukar tasiri ba a kan talakawan kasar waxanda galibinsu ke sayen kananzir xin a kan fiye Naira 100 kowacce lita a hannun ‘yan kasuwa. Kuma akwai matsalar rashin wadatarsa.