Hukumar Kula da Albakatun Mai (PPMC) ya sake kara farashin litar man fetur a karo na biyar cikin wata biyar a Najeriya.
Karin da gwamanti ta yi ya mayar da farashin kowace litar man fetur N172.17.
Hukumar a cikin wata sanarwa ta ce “Sabon farashin fetur zai fara aiki daga Juma’a 13 ga Nuwamba, 2020 a kan N155.17 ga manyan dillalai”.
Idan za a iya tunawa N151.56 ne farashin fetur da PPMC ta sanya wa manyan dillalai a watan Satumban 2020, gidajen mai kuma na sayarwa 158 zuwa N162.
A watan Mayu 2020 Hukumar Kayyade Farashin Albakatun Mai (PPPRA) ta kara farashin fetur zuwa tsakanin N121.50 da N123.50.
Daga baya a watan Yuli ta mayar kara shi ya koma N140.80 zuwa N143.80.
A watan Agusta 2020 hukumar ta sake kara farashin ya kai N145.86 zuwa N148.86.
Sai a watan Satumba da PPPRA ta kara farashin ya koma N158 zuwa N162 a kan kowace lita.