A yau Jumma’ar ne 2 ga watan Agusta na 2019 aka kammala jigilar maniyatan Jahar Katsina zuwa garin Madina. Jirgi na 6 kuma na karshe daga Jahar Katsina ya tashi da misalin karfe 5:40 na yamma daga filin jirgi sama na Umaru Musa Ƴar’aduwa dauke da maniyata 520 cikin su harda sauran duk wani mai ruwa da tsaki akan aikin Hajjin na bana.
Sai dai Babban Jojin Jahar Mai Shari’a Musa Danladi Abubakar wanda yana cikin maniyatan ya ja hankalin masu amfani da kafar sadarwa da su rika tabbatar da labari kafin su watsa don gudun tayarwa na gida hankali ko wadanda ke can kasa mai tsarki.