An kammala gasar wasanni a tsakanin rukunonin kungiyoyin wasanni daban-daban na Jihar Legas a filin wasa na Cibiyar Bunkasa Wasanni ta jihar Legas da ke unguwar Yaba a ranar Litinin din da ta gabata.
An gudanar da gasar ne tare da hadin gwiwar kungiyoyin wasanni naJjihar Legas da ma’aikatar matasa da wasanni da walwala na jihar da kuma ofishin da ke kula da bunkasa wasanni da ke ofishin gwamnan jihar.
A bangaren wasan damben Kareti, kungiyar Emma Martial Art Club ce ta lashe gasar inda ta samu lambar zinare biyar da azurfa uku da kuma tagulla 10.
kungiyar da ake kira I Do Karate Club ita ta zo na biyu inda ta lashe lambar zinare uku da azurfa uku da tagulla uku. Ita kuwa kungiyar Golden Academy Karate Club ita ta zo na uku tare da lashe azurfa biyu.
A bangaren wasan kwallon Badmintan Femi Bioku ya lallasa Seye Popoola a zagaye na karshe da maki 21-16 da kuma 21-16 wanda hakan ya sa ya zama zakara a rukunin maza zalla.
Bioku ya fadawa Aminiya cewa ya yi mutukar farin ciki da ya lashe gasar inda ya yi alkawarin zai dage domin ganin ya lashe gasar da za a gudanar a shekara mai zuwa.
Shi kuwa Popoola wanda bai sami nasara ba ya bayyana bakin cikinsa saboda rashin nasarar da ya samu sai dai ya ce zai kara kaimi domin ganin ya yi rawar gani a shekara mai zuwa.
A bangaren mata na kwallon Badimintan Tosin Solademi ce ta lallasa abokiyar hamayyarta Shade Akinyemi da ci 21-18 da kuma 21-17.
Tosin ta bayyana farin cikinta dangane da nasarar da ta samu yayin gasar a kan abokiyar hamaiyarta Shade.
Ta ce ‘Gaskiya na gamu da turjiya daga abokiyar karawata amma na gode Allah da Ya ba ni nasara’.
An kammala gasar wassanni ta bana a Jihar Legas
An kammala gasar wasanni a tsakanin rukunonin kungiyoyin wasanni daban-daban na Jihar Legas a filin wasa na Cibiyar Bunkasa Wasanni ta jihar Legas da ke…
